<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>276</hymn_number>
<title>Mai Bin Ubanginmu, Ka Kama Hanyarsa LW276</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mai Bin Ubanginmu, ka kama hanyarsa,
 Yesu ne ya ke kira, Yesu ne ladanka.

[V2]
 2) Ka yad da aikin duhu, ka tuƃe zunubi,
 Yi tseren nan gabanka tare da haƙuri.

[V3]
 3) Ba za ka ji Shaiɗan ba, ba za ka koma ba.
 Tare da Almasihu, bari ka ci gaba.

[V4]
 4) Raini ba za ka ƙi ba, kada ka ji tsoro.
 Ka dubi Almasihu, kullum ka shaida shi.

[V5]
 5) Mai Bin Ubangijinmu, ka dubi darajar
 Da aka sa gabanka, ka gama lafiya.</lyrics>
</song>